Monday, October 19, 2026
HomeTsaroMatawalle ya umarci sojoji su murƙushe ‘yan ta’adda a Arewa

Matawalle ya umarci sojoji su murƙushe ‘yan ta’adda a Arewa

Ƙaramin Ministan Tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya umarci dakarun sojin ƙasar da su ƙara kaimi wajen kakkabe masu tada ƙayar baya da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a yankin Arewa domin dawo da zaman lafiya.

Matawalle ya bayar da wannan umarni ne yayin da ya kai ziyarar jajantawa ga waɗanda hare-haren ‘yan bindiga na baya-bayan nan suka shafa a ƙaramar hukumar Bungudu da sauran al’ummomin da ke Jihar Zamfara.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da rashin tsaro, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki da dabarun da suka dace domin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan ta’adda.

Ministan ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.

Ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da bibiyar maharan har sai an gurfanar da su a gaban shari’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments