Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiNSCDC ta kama mutane 6 kan zargin lalata bututun man fetur a...

NSCDC ta kama mutane 6 kan zargin lalata bututun man fetur a Abuja

Rundunar Tsaro ta civil defense (NSCDC) ta kama mutane shida da ake zargi da lalata bututun mai tare da satar fetur a yankin Pagada, da ke Karamar Hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A cewar rundunar, an kama waɗanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 3:30 na dare ranar 18 ga Yulin 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukansu a kusa da bututun mai.

Rahotanni sun nuna cewa an cafke su ne yayin da suke dibar fetur cikin jarkoki bayan sun huda bututun da injin huda ƙarfe.

Rundunar ta kuma kwato babura biyu, jarkoki huɗu cike da fetur, shebur guda, bindigogi guda biyu, da injin huda ƙarfe da ake zargin an yi amfani da shi wajen aikata laifin.

Hukumar NSCDC ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ake zargi suna da hannu a wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments