Majalisar Dokokin Faransa na shirin amincewa da wani kudiri da zai haramta wa yara ‘yan kasa da shekara 15 amfani da kafafen sada zumunta.
Ana sa ran za a kada kuri’ar karshe kan kudirin a makonnan, bayan ‘yan majalisar dattawa da na wakilai sun cimma matsaya a kan batun ranar Litinin.
Idan aka amince da kudirin, Faransa za ta zama kasa ta farko a cikin Tarayyar Turai (EU) da ta kafa irin wannan takunkumi kan shekarun amfani da kafafen sada zumunta.
Matakin na zuwa ne yayin da ake kara muhawara kan illar amfani da kafafen sada zumunta ga yara, musamman dangane da lafiyar kwakwalwa, tsaro da kuma kare su daga abubuwan da ba su dace da shekarunsu ba.
Ministar Harkokin Fasahar Zamani ta Faransa, Anne Le Henanff, ta bayyana cewa matakin na da nufin kare yara ta hanyar kayyade shekarun da mutum zai fara amfani da kafafen intanet.
Ta ce Faransa na son zama kasa ta farko a Turai da za ta kafa ka’idoji masu tsauri kan shekarun amfani da kafafen sada zumunta.
Ana sa ran kudirin zai samu amincewar majalisar, duk da cewa jam’iyyun adawa na iya kalubalantar wasu sassan dokar.
Idan dokar ta samu amincewa, za ta zama daya daga cikin manyan matakan da wata kasa ta Tarayyar Turai ta dauka wajen takaita amfani da kafafen sada zumunta ga yara.