Sunday, October 18, 2026
HomeLabarai‘Yan ta’adda na amfani da fasahar zamani da kuɗin crypto wajen ƙarfafa...

‘Yan ta’adda na amfani da fasahar zamani da kuɗin crypto wajen ƙarfafa ayyukansu – MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yadda ƙungiyoyin ’yan ta’adda ke amfani da sabbin fasahohi, ciki har da jirage marasa matuƙi da hada-hadar kuɗaɗen crypto, wajen ƙarfafa ayyukan ta’addanci a Najeriya da wasu ƙasashen yankin Sahel.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yadda ƙungiyoyin ’yan ta’adda ke amfani da sabbin fasahohi, ciki har da jirage marasa matuƙi da hada-hadar kuɗaɗen crypto, wajen ƙarfafa ayyukan ta’addanci a Najeriya da wasu ƙasashen yankin Sahel.

Majalisar ta bayyana cewa ƙungiyoyin ’yan ta’adda na ƙara amfani da jirage marasa matuƙi wajen kai hare-hare da kuma sa ido kan wuraren da suke shirin kai wa farmaki.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, amfani da wannan fasaha na bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda damar faɗaɗa ayyukansu tare da ƙara ƙarfin kai hare-hare a Najeriya da sauran ƙasashen Sahel.

Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun munanan hare-haren ’yan ta’adda a yankin. A ƙarshen makon da ya gabata, wani hari a Mali ya yi sanadin mutuwar sama da sojoji 50.

Wakilin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Afirka ta Yamma da Sahel, Leonardo Simão, ya ce ƙungiyoyin ’yan ta’adda na ƙoƙarin ƙara faɗaɗa tasirinsu ta hanyar shiga harkokin tattalin arziki da amfani da sabbin hanyoyin samun kuɗi.

Majalisar ta kuma bayyana damuwa kan yadda ’yan ta’addan ke amfani da cryptocurrency wajen tara kuɗaɗen da ake amfani da su wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

A Najeriya, gwamnati ta fara ɗaukar matakai na sanya ido kan harkokin cryptocurrency domin gano tare da dakile duk wani amfani da ake yi da ita wajen gudanar da ayyukan haramtattu.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ƙara jawo hankali kan buƙatar ƙasashen yankin Sahel su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen dakile amfani da fasaha da sabbin hanyoyin kuɗi wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Masana na ganin cewa yayin da ci-gaban fasaha ke kawo sauƙi da dama a duniya, rashin kulawa da shi na iya bai wa ƙungiyoyin ta’addanci damar ƙara faɗaɗa hare-harensu da kuma jefa rayukan jama’a cikin haɗari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments