Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiRundunar ‘Yan Sandan Kano ta horas da jami’ai 200 kan sarrafa makamai

Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta horas da jami’ai 200 kan sarrafa makamai

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kammala horas da jami’ai 200 kan dabarun amfani da makamai da inganta ƙwarewar aikin tsaro, a wani mataki na ƙarfafa aikin tabbatar da doka da oda a jihar.

Horon, wanda ya ɗauki tsawon wata guda, an gudanar da shi ne a sansanonin rundunar kwantar da tarzoma (PMF) na 9 da ke Hotoro da na 52 da ke Challawa.

An koyar da jami’an dabarun tunkarar masu aikata laifuka, amfani da makamai bisa ƙa’ida, da kuma bin dokokin aikin ’yan sanda.

Da yake jawabi a wajen bikin rufe horon, mukaddashin Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, DCP Audu Sabo, ya ce rundunar ta himmatu wajen gina jami’ai masu ƙwarewa, jajircewa da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam yayin gudanar da aikinsu.

Ya bayyana cewa horon ya kuma mayar da hankali kan inganta alaƙa tsakanin jami’an tsaro da al’umma, tare da ƙarfafa bin ƙa’idojin kare haƙƙin jama’a a yayin gudanar da ayyukan tsaro.

DCP Audu Sabo ya buƙaci jami’an da suka amfana da horon su yi amfani da ilimin da suka samu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma cikin gaskiya, ƙwarewa da biyayya ga doka.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da shirya irin waɗannan horo domin ƙara inganta tsaro da zaman lafiya a Kano.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments