Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiTinubu ya gana da gwamnonin APC a Abuja

Tinubu ya gana da gwamnonin APC a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da wasu gwamnonin jam’iyyar APC guda shida a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Gwamnonin sun isa ofishin shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma.Ganawar ta ɗauki ƙasa da awa ɗaya, kuma babu wani daga cikinsu da ya yi magana da manema labarai bayan kammala zaman.

Waɗanda suka halarta sun haɗa da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi; na Edo, Monday Okpebholo; na Ekiti, Biodun Oyebanji; na Kogi, Usman Ododo; na Sokoto, Aliyu Sokoto; da na Kebbi, Nasir Idris.

An yi taron ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar sababbin matsalolin tsaro, da suka haɗa da satar ɗalibai da masu ibada a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

asu daga cikin jihohin da suka samu wakilci a taron—Kebbi, Sokoto da Kogi—sun sha fama da hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane don kuɗin fansa a watannin baya-bayan nan.

Matakan tsaron Tinubu a Najeriya

A ranar 26 ga Nuwamba, 2025 Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a kan harkokin tsaro a fadin Najeriya, inda ya umarci sojoji, ’yan sanda da hukumomin leƙen asiri su ƙara ɗaukar ma’aikata tare da hanzarta tura su bakin aiki.

Haka kuma ya umurci hukumomin tsaro da su mayar da hankali kan kare makarantu, gonaki da wuraren ibada, yayin da gwamnonin jihohi.

Taron ya zo ne mako guda bayan sauya Ministan Tsaro da kuma sabunta tattaunawa da ƙasashen waje kan samun goyon bayan yaki da ta’addanci.

Dukkanin gwamnonin sun yi gum da bakinsu bayan taron.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments