Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta gurfanar da direbobin motoci 123 a gaban kotu bisa zargin amfani da motoci marasa lambar rajista ko kuma rufe lambobin motocinsu ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da take yi na ƙarfafa tsaro a faɗin jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
Ya ce an ƙaddamar da aikin Operation Clean Plates ne domin hana masu aikata laifuka amfani da motocin da ba za a iya tantance su ba.
A cewarsa, jami’an ’yan sanda sun kama wani mutum mai suna Mahi Ibrahim a ranar 9 ga Yulin 2026 bayan ya yi ƙoƙarin tserewa da wata mota marar lamba.
Binciken da aka gudanar ya kai ga gano bindiga kirar Beretta, tabar wiwi, wuƙa, wayoyin lantarki, batir Lithium 120 da kuma wata mota da ake zargin ta sata ce.
CP Bakori ya ce an miƙa wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) domin ci gaba da bincike, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta faɗaɗa aikin Operation Clean Plates zuwa dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Ya kuma yi kira ga masu motocin da su tabbatar da cewa sun yi rajistar motocinsu yadda doka ta tanada tare da amfani da sahihiyar lambar mota.
Haka kuma ya roƙi al’ummar Kano su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin yaƙi da aikata laifuka.