Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiDSS ta saki 'yar jarida da aka tsare kan zargin aiki ba...

DSS ta saki ‘yar jarida da aka tsare kan zargin aiki ba bisa ka’ida ba

Kwamitin Ƙasa na Cibiyar ’Yan Jarida ta Duniya (IPI Nigeria) ya sanar da sakin ’yar jarida Zainab Sodiq, wadda Hukumar Tsaro ta DSS ta tsare saboda mallakar jirgin ɗaukar hoto mara matuƙi (drone).

Kwamitin Ƙasa na Cibiyar ’Yan Jarida ta Duniya (IPI Nigeria) ya sanar da sakin ’yar jarida Zainab Sodiq, wadda Hukumar Tsaro ta DSS ta tsare saboda mallakar jirgin ɗaukar hoto mara matuƙi (drone).

Sakataren IPI Nigeria, Ahmed Shekarau, ya ce an saki Zainab ga shugabannin ƙungiyar da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Juma’a, 10 ga Yuli, bayan ƙoƙarin shiga tsakani da ƙungiyar ta yi.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun tare ta ne a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar 6 ga Yuli yayin da take shirin tafiya da jirgin ɗaukar hoton. Daga baya an umarce ta da ta kai kanta hedikwatar DSS da ke Abuja, inda aka tsare ta saboda rashin takardar izinin mallakar irin wannan na’ura.

Shugaban IPI Nigeria, Musikilu Mojeed, ya yi maraba da sakinta tare da yabawa DSS kan amsa kiran da ƙungiyar ta yi. Ya ce duk da cewa hukumomin tsaro na da alhakin kare tsaron ƙasa, ya kamata su gudanar da aikinsu cikin mutunta haƙƙin ’yan jarida da sauran ’yan ƙasa.

IPI Nigeria ta kuma gode wa dukkan mutane da ƙungiyoyin da suka nuna damuwa kan tsarewar Zainab, tana mai jaddada aniyarta na ci gaba da kare ’yancin aikin jarida da tabbatar da tsaron ‘yan jarida cikin bin doka da mutunta haƙƙin bil’adama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments