Sunday, October 18, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun kama dattijo mai shekara 80 da wasu bakwai kan...

’Yan sanda sun kama dattijo mai shekara 80 da wasu bakwai kan kisan shugaban MACBAN a Benue

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue ta kama wani dattijo mai shekaru 80 da wasu mutum bakwai da ake zargi da hannu a kisan shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen jihar, Alhaji Ardo Risku Mohammed, da kuma Yakubu Isa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue ta kama wani dattijo mai shekaru 80 da wasu mutum bakwai da ake zargi da hannu a kisan shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen jihar, Alhaji Ardo Risku Mohammed, da kuma Yakubu Isa.

An kashe marigayin Mohammed da Yakubu Isa ne a ranar 1 ga Yuli yayin da suke dawowa daga wani taron tsaro da rundunar ’yan sanda ta shirya a ƙaramar hukumar Ohimini. Tuni dai rundunar ta kama wasu mutum 10 dangane da lamarin tun da farko.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ta ce sabbin kamen sun biyo bayan tattara bayanan sirri, zurfafa bincike da kuma ci gaba da samamen jami’an tsaro.

Ta bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Chief Morgan Ejaga mai shekaru 43, Chief Moses Anteyim mai shekaru 45, Chief John Ogli mai shekaru 58, Chief Yawuhu Adaji , Sylvester Ajonye mai shekaru 80, Aba Alexander Uloko mai shekaru 59, da Fidelis Iduma mai shekaru 45.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Benue, CP Cletus Nwadiogbu, ya yabawa jami’an bincike kan ƙoƙarinsu, yana mai tabbatar da cewa bincike na ci gaba, kuma duk wanda aka samu da hannu kai tsaye ko a kaikaice a kisan za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tanadin doka. Ya kuma buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments