An ruwaito cewa ɗan wasan tsakiyar fili na ƙasar Afirka ta Kudu, Jayden Adams, wanda ya wakilci ƙasarsa a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, ya rasu yana da shekaru 25 a duniya.
Ministan Wasanni na Afirka ta Kudu, Gayton McKenzie, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Adams, yana mai cewa ƙwallon ƙafar ƙasar ta rasa ɗaya daga cikin matasan ’yan wasanta masu hazaka. Sai dai bai bayyana musabbabin mutuwar ba.
Rundunar ’yan sandan yankin Western Cape ta tabbatar da cewa ta fara bincike bayan an gano gawar wani mutum mai shekaru 25 a wani gida da ke unguwar Schotschekloof a birnin Cape Town. Ta ce ana ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar.
An haifi Adams a Cape Town, inda ya fara sana’arsa ta ƙwallon ƙafa da Stellenbosch FC kafin ya koma Mamelodi Sundowns a watan Janairun 2025. A gasar cin kofin duniya ta 2026, ya buga dukkan wasannin rukuni uku na Afirka ta Kudu, amma bai taka leda ba a wasan da Kanada ta fitar da ƙasar daga gasar.
Rasuwar Adams ta zo ne kasa da wata guda bayan rasuwar kakarsa. Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta Kudu ta bayyana cewa duk da wannan babban rashi, ya taka leda a wasan da ƙasarsa ta yi da Czechia, inda ya nuna jajircewa duk da halin baƙin cikin da yake ciki.