Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn cafke matashi mai shekaru 23 kan zargin kashe Farfesa da kaninsa...

An cafke matashi mai shekaru 23 kan zargin kashe Farfesa da kaninsa a Benue

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Benue ta kama wani matashi mai suna Abdullahi Usman, mai shekaru 23, bisa zargin hannu a kisan wani malamin jami’a, Gabriel Saawua Nyityo, da kuma ƙaninsa, Iorngee John Nyityo.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Udeme Edet, ya ce jami’an ’yan sanda sun samu kiran gaggawa daga yankin Adaka da ke ƙaramar hukumar Makurdi, inda suka tarar da gawarwakin mutanen biyu.

Bayan gudanar da bincike na farko, rundunar ta kama Abdullahi Usman, ɗan asalin garin Awe na jihar Nasarawa, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano tare da cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe Farfesa Nyityo, mai shekaru 58, da ƙanensa mai shekaru 19 a gidansu da ke Adaka da sanyin safiyar ranar Laraba, 8 ga Yulin 2026.

Lamarin ya girgiza al’ummar jihar Benue da kuma Jami’ar Benue, inda marigayin ya kasance malami a Sashen Tarihi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments