Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAna ganin sakamako – Ndume ya bukaci Tinubu ya ci gaba da...

Ana ganin sakamako – Ndume ya bukaci Tinubu ya ci gaba da matsa wa ‘yan bindiga lamba

Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ci gaba da matsa wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda lamba.

Ya bayyana cewa idan aka ci gaba da irin wannan farmaki, Najeriya za ta shawo kan matsalar tsaro da ke kara ta’azzara.

Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa, Ndume ya bayyana cewa rashin tsaro shi ne babban matsala a Najeriya a halin yanzu.

Ya yaba wa Shugaba Tinubu, Rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa kara kaimi wajen yakar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, yana mai cewa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan na nuna ana samun ci gaba.

A cewarsa, an kashe wasu shugabannin ‘yan bindiga, yayin da wasu kwamandojinsu suka mika wuya kwanan nan, lamarin da ya ba shi kwarin gwiwar cewa za a kawo karshen matsalar idan aka ci gaba da wannan kokari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments