Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya karɓi baƙuncin gwamnonin Jihohin Arewa da Sarakunan Gargajiya na yankin, domin tattauna matsalolin tsaro da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya da ci gaban Arewa.
An gudanar da taron ne a Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, inda ya samu halartar Sarakunan Gargajiya ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, tare da sauran sarakunan gargajiya da kuma gwamnonin Jihohin Arewa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Haka kuma, manyan jami’an Gwamnatin Tarayya da shugabannin hukumomin tsaro sun halarci taron, ciki har da wakilan Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Ministan Tsaro, Sufeto Janar na ’Yan Sanda da Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS.
A yayin zaman, mahalarta taron sun tattauna kan halin da ake ciki na matsalolin tsaro a yankin Arewa, tare da duba hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnoni, sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro domin magance ƙalubalen da ke addabar yankin.
Taron ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai, musayar bayanan sirri da kuma aiwatar da dabarun da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da bunƙasa ci gaban yankin Arewa baki ɗaya.