Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Baba Tela, bisa rasuwar ‘ya’yansa biyu, Mustapha da Ummi, a wani hatsarin mota.
A cikin wata sanarwa, Kwankwaso ya bayyana cewa rasuwar ta jefa iyalan mamatan cikin babban baƙin ciki, tare da girgiza al’ummar Masarautar Katagum da ma jihar Bauchi baki ɗaya.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Bauchi da ɗaukacin al’ummar jihar, yana addu’ar Allah ya jiƙan Mustapha da Ummi, Ya gafarta musu kura-kuransu, sannan Ya bai wa iyalansu da ’yan uwansu haƙurin jure wannan babban rashi.