Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa wasu da ake zargi da damfarar intanet sun sace sama da Naira miliyan 7.2 daga asusun bankin wata alƙaliya a lokaci guda.
A cewarsa, kuɗin da aka sace su ne alƙaliyar ta tara tsawon shekara shida domin biyan kuɗin karatun ɗanta, lamarin da ya nuna irin illar da laifukan damfarar intanet ke haifarwa ga al’umma.
Olukoyede ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da wasu littattafai guda biyu da tsohuwar Alƙaliyar Babbar Kotu, Mai Shari’a Alaba Omolaye-Ajileye, ta wallafa.
Ya yi amfani da wannan misali wajen jaddada buƙatar ƙara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya daga masu aikata damfarar intanet, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin yaƙi da irin waɗannan laifuffuka.
Shugaban na EFCC ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen yaƙi da masu aikata laifukan damfara ta intanet da kuma kare dukiyoyin ’yan ƙasa.