Ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe sa’o’i ana yi a ranar Talata ya haddasa ambaliya a yankuna da dama na jihar Legas, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa tare da jefa mazauna wasu unguwanni cikin mawuyacin hali.
Ambaliyar ta shafe wasu manyan hanyoyi da unguwanni da suka haɗa da Victoria Island, Lekki, Ikeja, Gbagada, Mushin da Mafoluku, inda ruwa ya cika tituna tare da janyo tsaiko ga zirga-zirga.
Gwamnatin jihar ta buƙaci al’umma su kwantar da hankalinsu, tana mai tabbatar da cewa hukumomi na ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan da suka dace domin rage illar ambaliyar.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewa ruwan saman ya sauka da ƙarfi cikin ɗan gajeren lokaci, abin da ya sanya magudanan ruwa suka cika fiye da ƙarfinsu.
Ya ƙara da cewa ba Legas kaɗai ce ta fuskanci irin wannan yanayi ba, domin wasu sassan nahiyar Afirka da kuma Arewacin Amurka sun fuskanci irin wannan ruwan sama mai ƙarfi a kwanakin nan.
Gwamnatin ta sake yin kira ga mazauna jihar da su guji zubar da shara a magudanan ruwa tare da kauce wa gina gine-gine a wuraren da ke toshe hanyoyin ruwa, tana mai cewa hakan na daga cikin muhimman matakan rage haɗarin ambaliya a nan gaba.