Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiLabaraiSama da kwamandoji da manyan mayaƙan ISWAP 70 sun miƙa wuya a...

Sama da kwamandoji da manyan mayaƙan ISWAP 70 sun miƙa wuya a Borno

Sama da kwamandoji da manyan mayaƙan ƙungiyar ISWAP 70 sun miƙa wuya ga dakarun sojin Najeriya a jihar Borno, bayan ci gaba da hare-haren soji ta ƙasa da sama da suka raunana sansanonin ƙungiyar.

Rahotanni sun ce an tsare waɗanda suka miƙa wuya a wani wuri na musamman domin gudanar da bincike da tantancewa, yayin da hukumomin tsaro ke tattara bayanan sirri da za su taimaka wajen ci gaba da yaƙi da ta’addanci.

Sai dai ba a bayyana sunayensu ba saboda dalilan tsaro.

Majiyoyin tsaro sun danganta wannan nasara da ƙarin matsin lambar da rundunar Operation HADIN KAI ke yi kan sansanonin ISWAP, inda hare-haren suka lalata cibiyoyin jagoranci, wuraren ajiyar kayayyaki da hanyoyin samar da kayan tallafi, lamarin da ya tilasta wa wasu daga cikin mayaƙan ƙungiyar zubar da makamansu tare da miƙa wuya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments