Ofishin Jakadancin Ireland da ke Najeriya ya sanar da cewa za a buɗe neman guraben karatu na Ireland Fellows Programme 2026 daga ranar 29 ga Yuni, inda zai bai wa ’yan Najeriya damar yin karatun digiri na biyu (Master’s) a ƙasar Ireland tare da cikakken tallafi.
A cikin sanarwar da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa shirin ya shafi ƙwararrun ma’aikata masu tasowa daga Najeriya da Ghana da ke son yin karatun shekara ɗaya a manyan jami’o’in Ireland.
Masu neman gurbin dole ne su kasance ’yan Najeriya ko Ghana da ke zaune a ƙasashensu, su mallaki digiri na farko da aƙalla sakamakon Second Class Lower, tare da samun ƙwarewar aiki na aƙalla shekaru uku.
Ga masu neman gurbi daga Najeriya, shirin ya haɗa da Roger Casement Fellowship in Human Rights, wanda ya shafi fannonin Shari’a, Haƙƙin Dan Adam da Mulki.
Tallafin karatun ya haɗa da kuɗin makaranta, alawus na wata-wata, kuɗin masauki, tikitin jirgi, kuɗin biza da kuma inshorar lafiya.