Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiHarin Rasha ya afka wa jirgin dakon kaya na Turkiyya a ruwan...

Harin Rasha ya afka wa jirgin dakon kaya na Turkiyya a ruwan Ukraine

Rundunar sojin ruwa ta Ukraine ta ce harin ya samu ne ta amfani da jiragen sama marasa matuƙa, inda aka kai wa jirgin Victress, mai ɗauke da tutar Panama. A cewarta, ma’aikatan jirgin da suka jikkata sun haɗa da ’yan ƙasashen Masar, Turkiyya da Indiya.

Ukraine ta bayyana cewa an yi nasarar ceto dukkan mutanen da ke cikin jirgin ba tare da rasa rai ba, sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda suka jikkata ko girman raunukansu ba.

A wani ɓangaren kuma, hukumomin Rasha sun ce sun harbo jiragen sama marasa matuƙa da dama a safiyar Litinin, tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na ɗan lokaci a wasu filayen jiragen sama, bayan hare-haren da Ukraine ta kai kan wasu muhimman wurare a cikin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments