Gwamnatin Zamfara ta ce ta yi nasarar shawo kan ɓarkewar cutar kwalara da ta addabi al’ummomi da dama a ƙananan hukumomi 14 na jihar, tare da tabbatar da cewa yanzu babu wani sabon lamari na cutar a kowane yanki.
Cikin wata sanarwa daga ma’aikatar lafiyar jihar ta ce kwamishiniyar lafiya, Dr Nafisa Maradun, ta bayyana hakan yayin taron duba matakan da aka ɗauka wajen yaƙi da kwalara, da aka gudanar a cibiyar ayyukan gaggawa ta kiwon lafiya a Gusau.
A yayin bayanin yadda aka yaƙi cutar, Dr Nafisa ta bayyana cewa an samu adadin mutum 15,464 da suka kamu da kwalara, inda aka yi wa 15,265 magani kuma aka sallame su, yayin da mutum 192 suka rasa rayukansu a kananan hukumomi 14 na jihar.
Kwamishiniyar ta ce gwamnatin jihar ta samar da ingantaccen tsarin shirin kariya daga annoba domin magance duk wani barazana ga lafiyar jama’a nan gaba.
Waɗannan barazanar sun haɗa da kwalara da gudawa da sankarau da sauran cututtuka masu hatsari ga lafiyar al’umma.