Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSojoji da 'yan sanda sun ba hammata iska a bainar jama'a a...

Sojoji da ‘yan sanda sun ba hammata iska a bainar jama’a a Filato

Sojoji da yan sanda sun bawa hammata iska a tsakanin su bayan wata hatsaniya

Hatsaniya ta barke tsakanin sojoji biyu da ’yan sanda biyu a wata kasuwa a Ahmadu Bello Way, Jos, lamarin da ya jawo tashin hankali sosai.

Shaidu sun bayyana ce rikicin ya samo asali ne bayan wani soja ya fusata kan wani dillalin waya, inda rikicin ya rikide zuwa fada tsakanin jami’an tsaro.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da cewa an shawo kan lamarin, an hukunta wadanda suka yi kuskure, kuma an dauki mataki.

Lamarin dai ya razana jama’a, musamman ganin cewa rikicin ya afku tsakanin jami’an da ya kamata su kasance masu kula da tsaro da zaman lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments