An tabbatar da mutuwar akalla mutane 10 tare da jikkatar wasu bakwai bayan wata mota ta taka bam da aka binne a kan hanyar Bagega zuwa Anka a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 9 ga Yunin 2026, lokacin da wata motar Volkswagen Golf 3 Wagon da ke dauke da fasinjoji ta taka bam din da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa a kan hanyar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa da farko an tabbatar da mutuwar mutum daya da kuma jikkatar wasu bakwai.
Sai dai yayin da jami’an tsaro suka ci gaba da gudanar da bincike a wurin, an gano karin gawarwaki tara.
Bayan samun rahoton aukuwar lamarin, rundunar ‘yan sanda ta tura jami’an ta na musamman zuwa yankin domin gudanar da bincike da kuma tabbatar da tsaro.
Ana zargin cewa ’yan bindigar da ke addabar yankin ne suka dasa bam din domin kai hari ga matafiya da mazauna yankin.