Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiDalilan da suka sa gas din girki ya yi tashin gwauron zabo...

Dalilan da suka sa gas din girki ya yi tashin gwauron zabo – Rahoto

Yayin da farashin iskar gas ke ci gaba da tashi a Najeriya, wasu mazauna jihar Kano sun bayyana cewa sun fara komawa amfani da gawayi domin girki saboda tsadar gas da ke ƙara ƙamari.

A wata ziyara da ICONIC TIMES24 ta kai wasu wuraren sayar da gas, wani daga cikin manajojin gidan gas na Aliko, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa lalacewar hanyoyi sakamakon damuna na daga cikin manyan abubuwan da suka haddasa tashin farashin gas.

Ya ce motocin da ke jigilar gas na fuskantar matsaloli a kan hanyoyi, lamarin da ke ƙara tsadar sufuri kafin kayan su isa kamfanoni da wuraren sayarwa wanda hakan ne yasa aka fara samun karancin gas din a fadin Najeriya.

“Babbar matsalar da muke fuskanta yanzu ita ce lalacewar hanyoyi a lokacin damina.

Kafin gas ya iso wurinmu, ana ƙara kuɗin jigila saboda wahalar hanya.

“Kusan kullum farashin da ake kawo mana yana canzawa, na yau ya bambanta da na gobe,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa sanadiyyar tsadar gas din ta sanya a yanzu basa siyarwa da ma su sari su siyar a unguwanni.

A gefe guda kuma, wasu daga cikin masu amfani da gas sun nuna damuwarsu kan yadda farashin ke ƙaruwa kusan a kullum.

Wata mai amfani da gas ta ce tsadar da ake samu a halin yanzu ta su rage amfani da gas tare da komawa amfani da gawayi domin rage kashe kuɗaɗe.

Rahotanni sun nuna cewa ci gaba da hauhawar farashin gas sa mutane da dama komawa amfani da gawayi da itacen girki, lamarin da masana ke ganin zai iya ƙara matsin lamba ga muhalli da kuma lafiyar jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments