Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta kashe kusan Naira biliyan 6.6 a jihar Imo ta hanyar Shirin Tallafin Ci Gaban Iyalai da Ƙarfafa Tattalin Arziki, da nufin rage raɗaɗin talauci da inganta rayuwar al’umma.
Ministan Harkokin Jin Ƙai, Bernard Doro, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Owerri, babban birnin jihar Imo.
A cewarsa, shirin yana daga cikin manyan matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ɗauka domin tallafa wa iyalai masu rauni tare da fitar da su daga kangin talauci.