Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAbin da ya hana Kwankwaso da Obi dawo wa cikin jam'iyyarmu —...

Abin da ya hana Kwankwaso da Obi dawo wa cikin jam’iyyarmu — PRP

Baba Ahmed ya ce Kwankwaso da Obi sun nemi tikitin shugaban ƙasa ba tare da hamayya ba kafin shiga PRP

Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba Ahmed, ya bayyana dalilin da ya sa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ba su samu shiga PRP ba kafin zaɓen 2027.

Da yake magana a wani shirin siyasa na Hausa a gidan talabijin na DITV Kaduna, Baba Ahmed ya ce tattaunawar da aka yi tsakanin PRP da ‘yan siyasar biyu ta rushe ne bayan rashin jituwa kan sharuddan shiga jam’iyyar.

A cewarsa, Obi da Kwankwaso ne suka fara neman haɗin gwiwa da PRP, kuma har an kai matakin kafa kwamiti domin ci gaba da tattaunawa.

“Sun zo sun ce suna son shiga PRP, amma lokacin da muka zauna muka tattauna da su, akwai wasu buƙatu da suka gabatar,” in ji shi.

Shugaban na PRP ya ce ɗaya daga cikin manyan matsalolin shi ne yadda ‘yan siyasar biyu suka nemi a ba su tikitin takarar shugaban ƙasa ba tare da wata hamayya a cikin jam’iyyar ba.

“Tun kafin su shiga, sun ce su ne ‘yan takarar shugaban ƙasa, ma’ana a ba su tikitin kai tsaye. Muka ce a’a, wannan PRP ce, ba ma yin irin wannan siyasa,” in ji Baba Ahmed.

Ya ce jam’iyyar ta dage cewa dole Obi da Kwankwaso su fara shiga PRP a hukumance sannan su bi dokokin jam’iyyar kafin neman kowace kujera ta zaɓe.

“Na gaya musu cewa su fara shiga jam’iyyar. Bayan sun shiga, sai su ce ni Obi ne kuma ina son takarar shugaban ƙasa, ko ni Kwankwaso ne kuma ina son zama mataimakinsa.

“Amma ku zo tun kafin a yanke hukunci ku ce a tabbatar muku da tikiti ba tare da hamayya ba, idan da gaske kuna da ƙarfi, me ya sa kuke tsoron takara?” ya tambaya.

Baba Ahmed ya ce jam’iyyar ta san irin tasirin siyasar da kuma magoya bayan da Obi da Kwankwaso suke da su, amma ba za ta karya kundin tsarin jam’iyyar da tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida ba.

“Mun yi imanin cewa duk wanda ya ga Obi da Kwankwaso tare zai ga manyan ‘yan takara ne masu ƙarfi sun iso. Amma ba za mu karya dokokin jam’iyyarmu ba,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa bangarorin ‘yan siyasar biyu sun nemi a ba su manyan muƙamai a jam’iyyar saboda yawan magoya bayan da suke son kawowa PRP.

“Sun nemi a ba su muƙamai da yawa saboda sun ce suna da magoya baya masu yawa. Muka ce wannan ba matsala ba ce, ku fara shiga jam’iyyar sannan mu zauna mu tattauna,” ya ƙara da cewa.

Shugaban na PRP ya ce wasu matsaloli da suka haɗa da rashin ganin sunan jam’iyyar a shafin hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, da kuma rikice-rikicen cikin gida sun taimaka wajen rushewar tattaunawar.

“Sun ce lokacin da suka duba shafin INEC ba su ga sunan jam’iyyarmu ba, amma yanzu an gyara hakan. Sannan sun ji wasu mutane suna ikirarin cewa su ‘yan PRP ne, wanda suka ce zai iya jawo ruɗani idan suka shiga jam’iyyar. Muka gaya musu cewa muna ƙoƙarin magance matsalar,” in ji shi.

Sai dai Baba Ahmed ya ce bangarorin biyu sun rabu cikin lumana ba tare da wata matsala ba.

“Mun yi wa juna fatan alheri kuma muka rabu lafiya, babu wata gardama ko faɗa,” in ji shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments