Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGombe: Kotu ta yi watsi da karar da ke adawa da takaita...

Gombe: Kotu ta yi watsi da karar da ke adawa da takaita zirga-zirgar babura

Kotun ta tabbatar da cewa dokar takaita zirga-zirgar babura doka ce ta hana laifi

Gwamnatin Rundunar ‘Yan Sandan Gombe ta sanar da cewa Kotun Tarayya da ke jihar ta yi watsi da ƙarar da aka shigar a kanta, wacce ta nemi kalubalantar dokar takaita zirga-zirgar babura da aka kafa a matsayin matakin kare lafiyar jama’a da dakile aikata laifuffuka a jihar.

A sanarwar da rundunar ta fitar, mai dauke da sa hannun kakakinta, DSP Buhari Abdullahi an tunatar da cewa takunkumin ya fara aiki ne a ranar 12 ga watan Yuni, 2025 daga ƙarfe 7.00 na yamma zuwa 6.00 na safe.

Rundunar ta dauki matakin me sakamakon ƙarin matsalolin tsaro da aka rika fuskanta a birnin Gombe, inda aka gano cewa babura na taka muhimmiyar rawa a aikata laifuffuka daban-daban. An kafa dokar ne domin rage barazana ta hanyar ƙara tsaurara tsaro da inganta tsare-tsare na aiki.

Kotun ta tabbatar da cewa matakin ya yi daidai da ikon da kundin tsarin mulki ya ba rundunar ‘yan sandan Najeriya na kare rayuka da dukiyoyi, tabbatar da doka da oda da kuma dakile laifuka.

Rundunar, ƙarƙashin jagorancin CP Bello Yahaya, ta gode wa jama’ar jihar Gombe bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma.

Rundunar ta ce za a fitar da ƙarin bayani game da hukuncin kotun nan gaba kaɗan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments