Al’ummar dake zaune a ƙauyen Gurbi a karamar hukumar Kankara dake Jihar Katsina sun takawa wasu ’yan bindiga burki kan shiga garinsu a yammacin jiya Lahadi.
Wani mazaunin ƙauyen wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun isa tun da wuri, amma mutanen gari suka taru sannan suka tare su, suka hana su shiga cikin ƙauyen.
Bayan da ’yan bindigar suka gaza shiga garin, sai suka juya kan mutanen da ke gudun tsira da rayukansu.
Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun kasa shiga ƙauyen, amma sun kai wa mutanen da suka tsorata suka fara gudu hari.
Ko a kwana uku da suka gabata, maharan sun kai hari Zangon Kankara, inda suka ƙone gidaje biyu da mota guda tare da yin garkuwa da mutum biyu.