Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kashi biyu bisa uku na mutanen da ke fuskantar matsanancin karancin abinci a duniya a bara suna zaune ne a kasashe 10 kacal, inda kusan kashi daya bisa uku daga cikinsu ke Najeriya, Sudan da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Rahoton ya bayyana cewa rikice-rikice ne babban dalilin rashin wadatar abinci, tare da gargadin cewa matsalolin na iya ci gaba ko ma su tsananta a shekarar 2026 saboda rikici da sauyin yanayi.
Kasashen da abin ya fi shafa sun hada da Afghanistan, Bangladesh, Kongo, Myanmar, Najeriya, Pakistan, Sudan ta Kudu, Sudan, Syria da Yemen.
Duk da samun dan sauki a wasu kasashe kamar Bangladesh da Syria, rahoton ya ce hakan ya samu tangarda saboda tabarbarewa a wasu kasashe kamar Afghanistan, Kongo da Myanmar.
A karo na farko cikin rahoton, an tabbatar da yunwa mai tsanani a wurare biyu a lokaci guda — Gaza da wasu sassan Sudan.
Rahoton ya kuma nuna cewa mutane kusan miliyan 266 a kasashe 47 sun fuskanci matsanancin karancin abinci a bara, wanda ya kusan ninka adadin shekarar 2016.
Haka kuma, an gargadi duniya kan raguwar tallafin kasashen waje da kuma yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ke iya kara dagula al’amura, musamman ta hanyar kara yawan ‘yan gudun hijira da kuma tsadar taki.
Shugaban IFAD, Alvaro Lario, ya ce tashin farashin mai da taki zai iya yin mummunan tasiri ga noma da samar da abinci, musamman a lokacin shuka.
Ya bukaci a kara tallafa wa kananan manoma ta hanyar zuba jari a amfanin gona masu jure yanayi da kuma samar da taki a cikin gida, tare da karfafa jarin kamfanoni na cikin gida domin dorewar ci gaban noma.