Babbar Kotun Jihar Kogi da ke Lokoja ta yanke hukunci cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta biya tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, diyyar Naira biliyan 1 a wata shari’ar bata suna.
Hukuncin yana kunshe ne a cikin takardar hukunci da aka fitar ranar 23 ga Afrilu a Lokoja.
Kotun ta ce bisa hujjoji da aka gabatar, an yanke hukunci a bangaren mai kara. Alkalin kotun, Mai Shari’a A. S. Ibrahim, ya bayyana cewa kalaman da wadda ake kara ta yi a wani shirin talabijin na Arise TV mai suna “The Morning Show” a ranar 4 ga Nuwamba, 2022 sun bata sunan mai kara.
Kotun ta ce kalaman da ta yi, inda ta kira shi mai kisa, mai aikata miyagun laifuka da kuma barazana ga al’ummar Jihar Kogi, ba su da hujja.
Haka kuma kotun ta hana ta da dukkan wadanda ke tare da ita yin irin wadannan kalamai a nan gaba a gidajen rediyo ko talabijin.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa a biya Naira biliyan 1 a matsayin diyya ga mai kara.
Lauyan wadda ake kara ya kalubalanci ikon kotun na sauraron shari’ar, amma lauyan mai kara ya musanta hakan. Daga baya kotun daukaka kara ta yi watsi da korafin tare da tabbatar da cewa kotun Kogi na da ikon sauraron shari’ar.