Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNCDC ga yi gargaɗi kan ɓarkewar cutar sankarau saboda tsananin zafi

NCDC ga yi gargaɗi kan ɓarkewar cutar sankarau saboda tsananin zafi

Fargabar barkewar sankarau na ƙaruwa sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta a Najeriya.

Masana lafiya sun yi gargaɗin yiwuwar ɓarkewar cutar sanƙarau saboda tsananin zafin rana, inda su ka shawarci al’umma su riƙa ɗaukar matakan kaucewa faruwar hakan.

A cewar NCDC, zafin da ake ciki na iya haddasa barkewar cutar sankarau.

Masanan sun shawarci mutane su ƙauracewa shiga cunkuso idan dai ba ya zama dole ba, kana su rage yawan haɗuwa a daƙi guda, sannan su riƙa shan ruwa akai-akai.

Dama dai hukumar yaƙi da yaɗuwar cutuka ta yi gargaɗin kan yiwuwar ɓarkewar cutuka, da suka haɗa da kwalera da sauran cutuka.

Duk da cewa hukumar hasashen yanayi ta NIMET, ta yi hasashen samun saukar ruwan sama har ma da ambaliya a wasu jihohin ƙasar tsakanin 13 zuwa jiya 17 ga watan Afrilu, kawo yanzu dai babu rahotonnin saukar ruwan saman.

Tuni malaman addini suka fara kira ga al’umma da su fara addu’o’in roƙar ruwa ga Allah, ko za a samu sauƙin yanayin da ake ciki.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments