Wani sabon ce-ce-ku-ce ya ɓarke dangane da wasu tsoffin rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta da ake dangantawa da shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan.
Lamarin ya biyo bayan zargin cewa ya taba yin kalaman goyon bayan jam’iyyar APC a lokacin zaɓen 2023, duk da cewa INEC ta musanta wannan zargi.
Batun ya kara ɗaukar hankali ne bayan wani masani ɗan Najeriya da ke Amurka, farfesa Farooq Kperogi, ya wallafa wani rubutu inda ya ce wasu tsoffin sakonni daga wani asusun X da ake zargin na Amupitan ne sun nuna goyon baya ga APC da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kperogi ya bayyana cewa irin waɗannan sakonni na iya rage amincewar jama’a ga sahihancin hukumar zaɓe, har ma ya bukaci shugaban INEC ya yi murabus.
A cikin ɗaya daga cikin sakonnin da ake magana a kai, an ce an rubuta “Victory is sure!” a matsayin martani ga wani sakon shugaban matasan APC, Dayo Israel.
Wannan lamari ya jawo muhawara sosai a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin idan zargin ya tabbata, zai zama babban matsala ga gaskiyar aikin hukumar zaɓe.
Wasu kuma sun nuna shakku kan sahihancin zargin, suna cewa ba a tabbatar da cewa asusun na Amupitan ba ne, musamman ganin cewa an canza sunansa sau da dama.
Hukumar INEC ta sake nanata cewa zargin ƙarya ne, tana mai cewa shugaban nata ba shi da wani asusu a dandalin X, tare da gargadin jama’a kan masu amfani da sunayen bogi domin yaɗa ƙarya.