Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiBa sojoji ne ke sayen kayan aiki da kansu ba – Rundunar...

Ba sojoji ne ke sayen kayan aiki da kansu ba – Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin cewa sojoji na sayen kayan aiki kamar kayan sawa da rigunan kariya da kuɗinsu, tana mai cewa wannan batu ƙarya ne kuma yaudara ce.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa rundunar ta mayar da martani ne ga wani tsohon soja, Rotimi Olamilekan wanda ya yi zargin a wata hira da ta karade kafafen sada zumunta cewa sojoji na sayen kayan aiki da kansu duk da ƙarancin albashi.

A cikin sanarwar da jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar sojin Najeriya, Appolonia Anele, ta fitar, an bayyana cewa rundunar na da tsarin albashi mai kyau tare da alawus-alawus da ake biya kai tsaye ga sojoji, ciki har da alawus na kayan sawa da na ayyukan yaƙi a fagen daga.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments