Harin ‘yan bindiga a wurin ɗaurin aure a Kaduna ya janyo asarar rayuka 13 da kuma sace wasu mutane.
Mummunan harin da ‘yan bindigar suka kai ya tarwatsa wani ɗaurin aure a ƙauyen Kahir da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna a arewacin Najeriya, inda ya kashe aƙalla mutane 13 tare da garkuwa da wasu da dama.
Rundunar ‘Yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin da ya jikkata wasu mutane, tana mai cewa tana kan tattara bayanai game harin ciki har da adadain waɗanda aka sace.
Wani shugaban alu’umma, Musa Adamu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:47 na dare ranar Lahadi.
Ya ce maharan, waɗanda suka je da yawa ɗauke da muggan makamai, sun afka wa wurin inda suka fara harbin kan-mai-uwa-da-wabi ga baƙin cikin ɗakin taron.
Wasu daga cikin waɗanda suka halarci bikin sun ji rauni daga harbin bingida kuma an garzaya da su asibitin gwamnati da ke Kagarko, yayin da aka tura waɗanda rauninsu ya yi yawa asibitoci a birnin Kaduna.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigan sun shafe kusan sa’a ɗaya suna aika-aikar ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Rahotanni sun ce sun saci kayayyakin abinci da kayayyakin masaraufi a shagunan da ke kusa tare da ɗauke magunguna daga wani kantin magani.
Tuni dai aka fara neman maharan domin kama su da kuma hukunta su, in ji hukumomin ‘yan sanda.
Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Arewa Maso Yammacin ƙasar da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Sauran jhohin sun haɗa da Sokoto da Kaduna da Kebbi da Zamfara da kuma Katsina.