Wata babbar mota dauke da yashi ta yi karo da babbar ƙofar shiga gidan gwamnatin jihar Gombe a ranar Talata, lamarin da ya janyo mummunar ɓarna ga ginin.
Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 12:55 na rana.
Motar ta buge kofar da a yanzu ake aikin gina ta a matsayin wani ɓangare na gyare-gyaren da gwamnatin Gwamna Muhammadu Yahaya ke yi.
Har yanzu ba a ƙaddamar da ƙofar a hukumance ba.
Rahotanni sun nuna cewa motar ta kwace wa direban motar, ya kuma buge ƙofar da aka kashe kuɗi masu yawa wajen ginawa.
Ana zargin motar na kamfanin Tricata Nigeria Ltd ce, sai dai ba a samu lambar rajistarta a wurin da abin ya faru ba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Darakta janar na harkokin yaɗa labaran gwamnatin Gombe, Ismaila Misilli, ya ce babu wanda ya rasa ransa a hatsarin.
“Lamarin ya faru, amma muna gode wa Allah babu asarar rai. Direban kawai ya ji rauni kuma ana kula da lafiyarsa,” in ji shi.
A halin yanzu, ana ci gaba da manyan ayyukan gyare-gyare a hidan gwamnatin a matsayin wani ɓangare na ayyukan more rayuwa da ake yi a jihar.