Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiIran ta ce har yanzu tana shirye ta ci gaba da ganawa...

Iran ta ce har yanzu tana shirye ta ci gaba da ganawa da Amurka

Gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa tattaunawa da Amurka za ta ci gaba.

Manyan jami’an Amurka da na Iran na shirin ci gaba da tattaunawa bayan ganawar da suka yi ƙasar Oman kan batutuwan da ya haifar da fargabar ɓarkewar rikici tsakanin ƙasashen.

Ministan harkokin waje na ƙasar Iran, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar da aka shiga tsakani ta kasance “mafari mai kyau”, kuma an mayar da hankali kan ”batun nukiliya ne kaɗai”.

Ya ƙara da cewa a yanzu masu tattaunawa za su koma manyan biranen ƙasashensu domin tuntubar gwamnatocinsu.

Gabanin tattaunawar dai, jami’an Amurka sun ce suna son tattaunawa kan makamai masu linzami da Iran ke yi da kuma zargin da ta ke yi ma ta na goyon bayan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a yankin, wanda ya nuna gibin da ke tsakanin matsayin ƙasashen.

Gwamnatin Amurka dai ba ta ce komai kan batutuwan da aka tattauna ba.

Tattaunawar ta kai tsaye da aka yi a birnin Muscat ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara jibge sojojin Amurka a yankin Gabas ta tsakiya domin mayar da martani ga mumunar murƙushe masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Iran a faɗin ƙasar a watan da ya gabata, wanda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka ce ya kashe dubban mutane.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments