Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta kammala horar da sabbin jami’anta sama da 700 a wani gagarumin shirin horaswa mafi girma da aka gudanar a ’yan shekarun nan.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, DCF P.O. Abraham, ya fitar.
Ya bayyana cewa, bikin yaye jami’an ya gudana a ranar Alhamis 5 ga Fabrairu 2026 a makarantar horaswa ta NDLEA da ke birnin Jos na Jihar Filato.
Sanarwar ta kara da cewa jami’an sun samu horo kan kashe gobara, ayyukan ceto, jagoranci, ladabi da shirye-shiryen tunkarar gaggawa.
Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Olumode Samuel Adeyemi, ya ce horaswar na daga cikin matakan ƙarfafa ƙwarewa da shirya jami’ai domin fuskantar ƙalubalen gobara da bala’o’i a sassan ƙasar nan.