Wasu mutane da ba’a iya tantance ko su waye ba, sun hallaka ɗan tsohon shugaban ƙasar Libya Saif-al-Islam, bayan sun buɗe masa wuta a yammacin ƙasar.
Lauyan sa Khaled el-Zaydi ya tabbatar da kisan ga manema labarai a jiya Talata, duk da ya ke babu cikakken bayani a kan dalilan da suka haddasa kisan.
Ɗan tsohon shugaban ya kwashe shekaru ya na zama a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa, kafin lokacin da aka kama shi aka tsare har zuwa lokacin da ya kuɓuta zuwa lokacin da ya nemi tsayawa takarar shugabancin Libya.
RFI Hausa ta ruwaito cewa duk da yake ba shi da wani muƙami na gwamnati ya kasance ana kallon sa a matsayin mutum mai karfin faɗa a ji a ƙasar, wadda mahaifinsa ya kwashe shekaru sama da 40 yana jagoranci.