Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya na shirin horas da ’yan Najeriya miliyan 10 kan hada-hadar...

Gwamnatin Tarayya na shirin horas da ’yan Najeriya miliyan 10 kan hada-hadar kudi

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin horas da ’yan kasar miliyan 10 kyauta a fannin ilimin hada-hadar kudi da shigar da kowa cikin tattalin arziki, inda ta ce mayar da hankali kan matasa da mata shi ne mabuɗin cin gajiyar yawan al’ummar kasar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa da ke Abuja, yana mai cewa Najeriya ba za ta iya gina tattalin arziki mai karfi ba sai an gina kwarewa, gaskiya da basirar zamani.

A cikin sanarwar da Stanley Nkwocha, hadimi kan yada labarai na Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya fitar, ta ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) tsakanin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa da kungiyoyin kwararru guda shida, domin tsara horaswa, takardun shaidar kwarewa, da bunkasa basirar zamani ga ’yan kasa, musamman matasa da mata.

Sanarwar ta kara da cewa shirin, wanda ake aiwatarwa karkashin Kwamitin Shugaban Kasa kan Hada-hadar Kudi da Shigar da Kowa (PreCEFI), zai bai wa mahalarta ilimin zuba jari, sarrafa kasuwanci da amfani da fasahar zamani yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments