Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya isa Abu Dhabi dake Dubai domin halartar taron makamashi

Tinubu ya isa Abu Dhabi dake Dubai domin halartar taron makamashi

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar wani taron makon makamashi.

Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya samu tarba daga ministan harkokin wajen ƙasar UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, da jakadan UAE a Najeriya a ƙasar, Salem Saeed Al-Shamsi.

Shugaban Tinubu ya isa Abu Dhabi ne daga Turai, inda ya yi wani ɓangare na hutunsa ƙarshen shekara, inda ya tattauna da shugaban ƙasashen Rwanda da na Faransa, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Fadar shugaban Najeriya ta ce sarkin UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci Tinubu taron, wanda shugabannin duniya da ƙwararru da ƙungiyoyin fararen hula ke tattauna batutuwan da suka shafi makamashi da yadda za a inganta shi.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments