Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da shirinta na sakin mutane 70 da ake zargi da ta’addanci.
Gwamnatin ta ce yarjejeniyar ta taimaka wajen ceto mutane da dama da mahara suka sace.
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana dalilin da ya sa take shirin sakin mutum 70 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi ta’addanci.
Gwamnatin ta ce matakin yana daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da ta ƙulla da masu ɗauke da makamai a jihar.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya ce sakin mutanen zai taimaka wajen ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin al’ummomin da abin ya shafa da kuma ’yan bindiga da suka ajiye makamai.
Mu’azu, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da DCL Hausa a ranar Asabar, bayan da jama’a suka nuna fushinsu kan wata wasiƙa da ta nuna cewa gwamnatin jihar ta nemi kotu ta taimaka wajen sakin mutanen da ake tuhuma.
A cewarsa, yarjejeniyar zaman lafiyar ta shafi ƙananan hukumomi 15, kuma ta taimaka wajen ceto kusan mutum 1,000 da ’yan bindiga suka sace.
Ya kwatanta matakin da abin da ke faruwa a lokacin yaƙi, inda ɓangarorin da ke faɗa da juna ke musayar fursunoni.