Wasu mambobin ADC ƙarƙashin ƙungiyoyin Forum of ADC Candidates da United Friends for Atiku (UFFA) sun kai ƙorafi ga ofishin jakadancin Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya kan zargin nuna son kai a ɓangaren shari’a.
Ƙungiyar ta kuma gudanar da zanga-zanga a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin jinkirin fitar da sahihin kwafin hukuncin da ya soke kwamitin gudanarwa na ƙasa na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.
A cikin wasiƙar ƙorafin da suka rubuta ranar 10 ga Nuwamba, 2026, sun bayyana cewa ba su amince da hukuncin kotun ba, don haka suka ɗaukaka ƙara domin neman a sake duba shi.
Mai gudanar da ƙungiyar, Audu Aliyu, ya ce lauyoyinsu sun nemi sahihin kwafin hukuncin bayan an yanke shi ranar 5 ga Nuwamba, tare da biyan kuɗin da ake buƙata.
Sai dai ya yi zargin cewa duk da yawan ziyartar ofishin rajistar kotun, har zuwa safiyar Talata ba a miƙa musu takardar ba. Ya kuma zargi wasu da matsa wa INEC lamba ta ɗauki mataki kan hukuncin da ba a bai wa jam’iyyar kwafinsa ba.
Ƙungiyar ta ce wannan jinkiri na iya tauye wa ADC damar amfani da haƙƙinta na ɗaukaka ƙara. Ta kuma bayyana cewa dimokuraɗiyya na iya fuskantar barazana ta hanyar jinkirin hukumomi da hana mutane samun damar yin adalci.
Aliyu ya jaddada cewa zanga-zangar ba ta da nufin raunana kotuna, illa dai kare bin doka da oda. Ya ce sun aika kwafin ƙorafin ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, NJC, NBA, Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, ECOWAS, Majalisar Ɗinkin Duniya, Tarayyar Turai da ofisoshin jakadancin Amurka.