Wata tsohuwar ma’aikaciyar bankin Jaiz, Habiba Abdulrahman, na fuskantar zargin damfarar kwastomomi 12 da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 104 a reshen bankin da ke Jos, jihar Plateau.
Rahoton binciken ’yan sanda ya ce Habiba ta karɓi kuɗin kwastomomin da sunan saka su cikin asusun ajiyar kuɗi na musamman, amma ta ƙirƙiri takardun shaidar bogi tare da amfani da sa hannunsu ba tare da izininsu ba.
’Yan sanda sun kuma zarge ta da tura kuɗin zuwa asusun mijinta, Manir Murtala, da ƙanwarta, Zainab Abdulrahman. Binciken ya nuna cewa ba a buɗe asusun ajiyar kuɗin da ta yi ikirarin samar wa kwastomomin ba, kuma an gano takardun bankin na bogi a gidanta.
An ce bankin ya sallami Habiba a watan Janairun 2026 bayan gano wasu kura-kurai, sannan aka kama ta bisa ƙorafin da manajan reshen bankin ya shigar. Daga bisani, ’yan sanda suka bayar da belinta bisa dalilan rashin lafiya.
A ranar Litinin ne kwastomomin da abin ya shafa suka gudanar da zanga-zanga suna neman a mayar musu da kuɗinsu. Sai dai lauyan bankin ya ce sun yi mu’amala da tsohuwar ma’aikaciyar ne kai tsaye, yayin da Habiba ta shaida wa wakilin jaridar cewa za ta bayyana nata ɓangaren nan ba da jimawa ba.