Ma’aikatar Harkokin Waje ta Tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa hukumomin tsaron ƙasar na ci gaba da yin aiki tare da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, domin fuskantar barazanar ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi da ke jawo husuma a ƙasa.
Ma’aikatar ta bayyana cewa wannan haɗin gwiwa ta tsaro, wadda ake gudanarwa bisa ka’idojin duniya da fahimtar juna tsakanin ƙasashe, ta haɗa da musayar bayanan sirri, tsara dabarun aiki, da sauran tallafi da ke mutunta ikon ƙasa da dokokin ƙasa da ƙasa.
Ta ce sakamakon haka ne aka samu kai hare-haren sama daidai kan wuraren ‘yan ta’adda ke zaune a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa duk wani mataki na yaƙi da ta’addanci ana yin sa ne da nufin kare rayukan fararen hula, tabbatar da haɗin kan ƙasa, da kuma kare haƙƙi da mutuncin ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.
Ta ce duk wani nau’in tashin hankali na ‘yan ta’adda—ko a kan Kiristoci, Musulmi, ko wasu al’umma—barazana ce ga ƙimar Najeriya da kuma zaman lafiyar duniya.
Har ila yau, Najeriya na ci gaba da aiki tare da abokan hulɗarta ta hanyoyin diflomasiyya da tsaro domin raunana ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, katse hanyoyin samun kuɗinsu da kuma hana barazanar da ke ketare iyakoki, tare da ƙarfafa hukumomin tsaro da na leƙen asiri na cikin gida.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da abokan hulɗa masu ruwa da tsaki, tare da sanar da jama’a ta hanyoyin hukuma a duk lokacin da ya dace.