Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiBabu abin da zai faru idan Atiku bai tsaya takara a zaben...

Babu abin da zai faru idan Atiku bai tsaya takara a zaben 2027 ba – Keyamo

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce Najeriya ba za ta shiga wani hali ba idan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce Najeriya ba za ta shiga wani hali ba idan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba.

Keyamo ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya rushe shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin David Mark, tare da soke matakan tsayar da ’yan takararta.

Ya tuna da hukuncin Kotun Ƙoli da ya soke nasarar APC a Bayelsa da Zamfara, wanda ya bai wa PDP damar karɓar mulkin jihohin a wancan lokaci.

Ministan ya ce APC ta amince da waɗancan hukuncin ba tare da kai wa kotuna hari ba. Ya kuma ambato Atiku yana cewa ya kamata ’yan siyasa su amince da hukuncin kotu maimakon sukar alƙalai.

Keyamo ya ce bai kamata a tsoratar da alƙalai ko yi wa ɓangaren shari’a barazana saboda hukuncin da bai yi wa wasu ’yan siyasa daɗi ba.

Ya ƙara da cewa, “Babu abin da zai faru idan Atiku Abubakar bai kasance cikin ’yan takarar zaɓen 2027 ba.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments