Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiBauchi: Limamin da aka zarga da goyon bayan Tinubu ya nemi afuwa

Bauchi: Limamin da aka zarga da goyon bayan Tinubu ya nemi afuwa

Malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dahiru Abubakar, wanda aka fi sani da Malam Danmalam, ya nemi afuwar jama’a bayan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan zargin cewa an cire shi daga mukaminsa saboda goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dahiru Abubakar, wanda aka fi sani da Malam Danmalam, ya nemi afuwar jama’a bayan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan zargin cewa an cire shi daga mukaminsa saboda goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Rahotanni sun bayyana cewa an cire malamin daga matsayin babban limamin wani masallaci da ke unguwar Madina a Bauchi, bayan ya nuna goyon bayansa ga shirin Tinubu na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Lamarin ya jawo muhawara a tsakanin jama’a, inda Hukumar Shari’a ta jihar Bauchi ta gayyaci malamin domin ya yi karin bayani kan kalaman da ya yi.

A yayin ganawar, Abubakar ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da karkatar da maganganunsa, yana mai cewa masallacin da ake magana a kai ƙarami ne, ba masallacin Juma’a ba, kuma ba shi da masu ibada da yawa.

Ya bayyana cewa masallacin yana da layukan sallah biyu kacal, kuma mutum bakwai ne ke gudanar da ibada a cikinsa.

Malamin ya nemi afuwar duk wanda ya fahimci kalamansa ta hanyar da ba daidai ba, yana mai cewa bai yi niyyar ɓata wa kowa rai ko tayar da muhawara a ƙasa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments