Saturday, November 7, 2026
HomeLabarai2026 na iya zama shekara ta biyu mafi zafi a tarihi –...

2026 na iya zama shekara ta biyu mafi zafi a tarihi – EU

Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta yi hasashen cewa shekarar 2026 za ta kasance ta biyu mafi zafi da aka taɓa samu a tarihi, bayan shekarar 2024.

Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta yi hasashen cewa shekarar 2026 za ta kasance ta biyu mafi zafi da aka taɓa samu a tarihi, bayan shekarar 2024.

Hukumar sa ido kan sauyin yanayi ta Copernicus ta ce akwai yiwuwar yanayin zafin duniya a bana ya kai ko ya zarce na shekarar 2024, wadda ita ce mafi zafi da aka taɓa samu.

Hukumar ta kuma bayyana cewa matsakaicin zafin duniya a watan Oktoba ya haura ma’aunin da aka samu kafin zamanin juyin juya halin masana’antu da digiri 1.75 a ma’aunin Celsius, lamarin da ya sanya watan ya zama mafi zafi a tarihin Oktoba.

Ta danganta ƙarin zafin da tasirin sauyin yanayi da ayyukan ɗan Adam, tare da ƙaruwar tasirin yanayin El Niño, wanda ke ƙara ɗumamar ruwan tekun Pacific tare da haddasa sauye-sauyen yanayi.

Masana sun yi gargadin cewa El Niño na iya taimakawa wajen sanya shekarar 2027 ta zama mafi zafi a tarihi, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce duniya na gab da kasa cimma burin yarjejeniyar Paris na takaita ɗumamar yanayi zuwa digiri 1.5 a ma’aunin Celsius.

Masana kimiyya sun jaddada cewa rage fitar da hayaki mai gurɓata muhalli daga makamashin burbushin halittu shi ne hanya mafi muhimmanci wajen rage illolin sauyin yanayi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments