Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiTun da wa’adin Tinubu ya zo karshe bai kamata ya ci gaba...

Tun da wa’adin Tinubu ya zo karshe bai kamata ya ci gaba da ciyo bashi ba – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman amincewar Majalisar Dattawa domin karɓo sabon bashin dala biliyan 7.7, kwatankwacin naira tiriliyan 10.79.

Atiku ya bayyana cewa bai kamata Majalisar Dattawa ta amince da wannan buƙata ba, musamman ganin cewa wa’adin mulkin gwamnatin Tinubu ya kusa ƙarewa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana matsayinsa ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓensa na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar a madadinsa.

A cikin sanarwar, Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da ci gaba da neman ƙarin rance ba tare da bayyana yadda aka yi amfani da basussukan da aka karɓa a baya ba.

Ya buƙaci Majalisar Dattawa ta yi cikakken bincike kan ayyukan da za a gudanar da kuɗaɗen, kuɗin ruwa, sharuddan karɓar bashin da kuma tsarin biyan sa kafin ta yanke shawara kan buƙatar shugaban ƙasar.

Haka kuma, Atiku ya yi kira ga hukumomin bayar da lamuni na ƙasashen waje da su dakatar da ba Najeriya ƙarin bashi har sai gwamnati ta bayyana cikakkun bayanai kan yadda za ta gudanar da sabon shirin karɓar bashin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments