Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da shawarar farfaɗo da shirin kamfanin jirgin saman ƙasa, Nigeria Air, tana mai cewa ci gaba da tattaunawa kan shirin ba zai haifar da wani amfani ba.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan bayan muhawara kan kudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar a zaman majalisar ranar Talata.
Duk da haka, majalisar ta ce Najeriya na buƙatar kamfanin jirgin sama na ƙasa, inda ta buƙaci Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta nemo sabuwar hanyar kafa shi.
Sanatocin sun kuma nemi gwamnatin tarayya ta tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da China, domin bai wa kamfanonin Najeriya damar tashi kai tsaye zuwa ƙasar.
Sanata Abdul Ahmed Ningi ya buƙaci a sake duba yarjejeniyar idan China ba ta bai wa kamfanonin Najeriya irin damar da take bai wa nata ba, yayin da Akpabio ya jaddada buƙatar samun kamfanin jirgin sama na cikin gida mai ƙarfi.