Wasu ’yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda biyar a wani harin kwanton ɓauna da suka kai wa ayarin motocin jami’an tsaro a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau, a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ’yan sandan na kan hanyarsu daga Sokoto zuwa Zamfara domin gudanar da wani aiki na musamman, lokacin da maharan suka buɗe musu wuta.
Wani jami’in ɗan sanda da ya tsira daga harin ya ce suna tafiya ne cikin motoci uku, lokacin da ’yan bindigar suka farmaki motar da ke ƙarshen ayarin.
Kakakin ofishin Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda mai kula da Shiyya ta 10 da ke Sokoto, Abdullahi Faruk, ya tabbatar da mutuwar jami’an tsaro biyar sakamakon harin.
Ya ce an kai gawarwakin jami’an zuwa ɗakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto.
Rahotanni sun kuma nuna cewa jami’an na kan hanyarsu ne domin gudanar da aikin samar da tsaro a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.