Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiMakinde ya fi Tinubu da sauran ’yan takara cancanta – Daura

Makinde ya fi Tinubu da sauran ’yan takara cancanta – Daura

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Alhaji Lawal Daura, ya ce Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya fi sauran ’yan takara cancanta da sahihanci wajen jagorantar Najeriya a zaɓen 2027.

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Alhaji Lawal Daura, ya ce Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya fi sauran ’yan takara cancanta da sahihanci wajen jagorantar Najeriya a zaɓen 2027.

Daura ya bayyana hakan ne yayin da shugabannin ƙungiyar Northern Patriotic Front (NPF) suka ziyarci hedikwatar yaƙin neman zaɓen APM a Abuja, inda suka karrama Makinde tare da bayyana goyon bayansu ga takararsa.

Ya ce gwamnatin Makinde da shi za ta mayar da hankali kan farfaɗo da tattalin arziki, inganta ilimi, samar da tsaro da haɗin kan ƙasa cikin wa’adin shekaru huɗu.

Daura ya buƙaci ’yan Najeriya su guji nuna bambancin ƙabila, su mayar da hankali kan ayyukan da ’yan takara suka gudanar a baya. Ya ce nasarorin Makinde a kasuwanci da mulkin Oyo, tare da gaskiya da riƙon amana, sun bambanta shi da sauran ’yan takara.

A nasa jawabin, shugaban NPF, Alhaji Ali Abacha, ya tabbatar da goyon bayan masu ruwa da tsaki a Arewa ga Makinde, yana mai cewa ayyukansa a Oyo sun ƙarfafa musu gwiwar mara masa baya.

Abacha ya kuma yaba wa Makinde bisa zaɓen Daura, ƙwararre kan harkokin tsaro, a matsayin abokin takararsa. Ya ce ƙungiyar za ta yi aiki tukuru domin ganin tikitin Makinde da Daura ya yi nasara a zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments